'Yan sandan Afirka ta Kudu sun wargaza zanga-zanga
February 13, 2022Talla
'Yan sandan kwantar da tarzoma a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu sun yi amfani da harsashen roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin ayyukan da baki ke yi a kasar.
Daruruwan mutanene suka fito zanga-zangar ta yau, sai dai jami'an tsaro sun yi nasarar tarwatsasu, yayin da suka tunkari wasu shagunan baki a birnin na Johannesburg.
Kasar ta Afirka ta Kudu da ke zama kasa mafi ci-gaban masana'antu a nahiyar Afirka tana samun mutane daga kasashe a nahiyar da ke zuwa domin neman aiki, sai dai suna cin karo da kalubalen tsana da tsangwama gami da kin jinin baki.