Wanzuwar rikici a garin Kidal na kasar Mali | Labarai | DW | 30.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wanzuwar rikici a garin Kidal na kasar Mali

'Yan tawayen Mali sun bayyana sake daukar makamai domin yakar gwamnati

'Yan awaren kasar Mali sun kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude ta watanni biyar da suka kulla tare da gwamnatin kasar, kana sun sake daukar makamansu, bayan wasu rigingimun da aka samu a garin Kidal da ke yankin arewacin kasar. Ayyana wannan kudirin, ya zo ne yini daya kachal bayan da dakarun gwamnatin Mali suka yi fito na fito da masu zanga zangar da suka hana fira ministan kasar shiga garin Kidal yayin wata ziyarar da ya shirya yi a garin, wanda ke zaman sansani ne ga 'yan tawayen. Kazalika, matsalar ta biyo bayan zagaye na farko ne na zaben majalisar dokokin kasar da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata. Yawan wadanda suka jefa kuri'a a lokacin zaben dai, ba su kai kaso 40 cikin 100 na wadanda suka cancanci jefa kuri'a ba, kuma a watan gobe - idan Allah ya kaimu al'ummar kasar Mali za ta je rumfunan zabe domin gudanar da zagaye na biyu na zabukan majalisar dokokin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman