Wanzar da zaman lafiya a Kongo | Labarai | DW | 07.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wanzar da zaman lafiya a Kongo

Gwamnatin Kongo ta bayyana tsara matakan daidaita matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo Joseph Kabila, ya lashi takobin tabbatar da kasancewar kasar tsintsiya madaurinki daya, daidai lokacin da 'yan tawayen da ke gabashin kasar ke ci gaba da tada kayar baya.

Shugaba Kabila ya ambata hakan ne a wannan Asabar din (07. 09. 13), a wani jawabi da yayi ga al'ummar kasar a wajen wani taro na wanzar da hadin kan kasa, inda ya ce sojin gwamnati za su tashi tsaye wajen ganin sun kare kasar, kana ya yi Allah wadai da masu son dagula lamura a kasar.

Kabila ya kara da cewar gwamnatinsa za ta yi bakin iyawarta wajen ganin an cimma matsaya a tattaunawar samar da zaman lafiya a kasar, wanda a ke yi a birnin Kampalan kasar Uganda.

A baya dai irin wannan tattaunawa ta samar da zaman lafiya tsakanin gwamnatin Kongo da 'yan tawayen kasar na M23, ta ci karo da matsaloli tun bayan da 'yan tawayen da a ke zargin na samun tallafin kasar Rwanda suka sake daukar makamai.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh