1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaOceania

Wani mutum dauke da wuka ya kashe mutane 6 a Australia

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 13, 2024

Kwamishiniyar 'yan sandan birnin New South Wales Karen Webb, ta ce babu tabbacin cewa ko harin ta'addanci ne mutumin mai shekaru 40 ya kai, amma dai 'yan sanda na ci gaba da bincike a kansa

https://p.dw.com/p/4ej3e
Hoto: Steven Saphore/AP Photo/picture alliance

Wani hari da wuka a birnin Sydney na kasar Australia ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, ciki har da jariri 'dan wata 9 a Asabar din nan, inda wasu guda 8 kuma suka samu raunuka.

Karin bayani:An kama dan Ostiraliya kan laufin cin zarafin 'yara 91

To sai dai wata 'yar sanda da ta tunkare shi gaba-gadi, ta samu nasarar harbe maharin har lahira, inda ta samu yabo da jinijna daga al'ummar kasar sakamakon wannan kokari.

Karin bayani:Ana zaben kasa a Australia

Kwamishiniyar 'yan sandan birnin New South Wales Karen Webb, ta ce babu tabbacin cewa ko harin ta'addanci ne mutumin mai shekaru 40 ya kai, amma dai 'yan sanda na ci gaba da bincike a kansa.

Hotunan nau'aurar kurilla da jami'an tsaro suka dauka sun nuna mutumin sanye da rigar kwallon Rugby ta gasar kasar ta Australia dauke da zaftareriyar wuka a hannunsa yana caccakawa mutane suna faduwa jina-jina.