Wani fadan Cocin Scotland ya yi marabus | Labarai | DW | 25.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani fadan Cocin Scotland ya yi marabus

Kardinal Keith O'Brien ya sanar da cewar ba zai kaɗa ƙuri'a ba a zaɓen sabon jagoran ɗariƙar Roman Katolika.

An ba da rahoton cewar wani babban limamin Cocin Roman Katolika na Scotland,kardinal Keith O'Brien wanda ake zargi da mumunar hallaya na yin ba daidai ba ga sauran fadan Cocin tun shekaru 30 da suka wucce .

Wanda kuma ke ɗaya daga cikin Kardinal ɗin da zasu tattaru domin zaɓen sabon jagoran yan ɗarikar Roman Katolika a ranar alhamis mai zuwa, ya yi marabus.A cikin wata sanarwa da ta baiyana Cocin Katolika ta Scotland ta ce tun a ranar 18 ga wannan wata, Paparoma Benedikt na 16 ya amince da takardar marabus ɗin ta limamin, wanda shi ne mafi girma a Cocin na Katolika a Ingila.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh.