Wani ɗan Liberia ya mutu da cutar Ebola a Najeriya | Labarai | DW | 25.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani ɗan Liberia ya mutu da cutar Ebola a Najeriya

Mutumin ɗan kimanin shekaru 40 ya mutu ne a wani asibitin na birnin Lagos inda ya kwashe kwanaki uku yana yin jinya.

Hukumomin a Najeriya sun tabbatar da mutuwar wani ɗan Liberia wanda ya kamu da cutar Ebola. Ministan yaɗa labaru na Najeriyar Labaran Maku ya bayyana matakan da aka ɗauka domin kare yaɗuwar cutar daga wannan mutumin. A lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai, wanda ya ce ana gudanar da bincike a kan iyakokin ƙasar.

wannan shi ne karo na farko da cutar ta ɓula a Najeriya ,wacce ta kashe mutane sama ɗari shida tun lokacin da ta ɓarke a ƙasashen Gini da Liberia.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar