Wanene za′a zaba ya zama sabon Paparoma? | Zamantakewa | DW | 13.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wanene za'a zaba ya zama sabon Paparoma?

Bayan murabus na Paparoma Benedikt na 16, an shiga muhawara a game da wanda zai gajeshi kan kujerar shugabancin yan darikar Katholika a duniya

Shin a wannan karo ma za'a zabi sabon Paparoman ne daga nan Turai. Ko wadanda suke da alhakin wannan zabe zasu nuna karfin zuciya, su zabi dan takara daga wata nahiyar dabam? Akwai yan takara masu yawa da ake ambata sunayensu a neman kujerar ta Paparoma. Akwai dan kasar Brazil Odilo Scherer da dan Kolumbia Salazar Gomez da dan kasar Ghana Peter Turkson. Masana da masu sharhi suna kuma ganin cewar zaben sabon Paparoman yana nufin zaben sabuwar alkibla ce da cocin na Katholika zai bi zuwa gaba a aiyukan sa.

Akwai bukatu iri dabam dabam da ake baiyanawa tun kafin zaben. Babban limanin birnin Cologne, Kardinal Joachim Meisner alal misali, yace yana dora muhimmanci ga zaben Paparoma mai cikakken koshin lafiya. Duk wanda za'a zaba kada ya wuce shekaru 70 da haihuwa, ya kasance mai matukar kwazo da fasaha da cikakken ilimi, kamar shi kansa Paparoma mai murabus, Joseph Ratzinger wato Benedikt na 16. Inda so samu ne, inji Meisner, da Paparoman da za'a zaba ya zama rabinsa marigayi Paparoma John Paul na shidda ne, rabinsa kuma Benedikt na 16. Shugabannin cocin Katholika daga kasashen Afirka sun baiyana cewar abin dake da muhimmanci fiye da inda sabon Paparoman zai fito, shine yadda zai tafiyar da sabon nauyin da za'a dora masa. Archbishp Ignatius Kaigama, shugaban limaman kirista na Katholika a Najeriya, kuma Archbishop na Jos, yace inda za'a zabi Paparoma daga Afirka da al'amarin yayi kyau, to amma wannan ba shine abin da mabiyar darikar Katholika a Afrika din suke dorawa muhimmanci ba.

O-ton Kardinal Kaigama(Hausa)

Papst mögliche Nachfolge von Papst Benedikt XVI Kardinal Francis Arinze

Cardinal Peter Turkson dan takarar neman kujerar Paparoma

Manyan limaman na cocin Katholika, suna da dalilinsu na neman a zabi sabon Paparoma da shekarunsa basu cika nisa ba. A watan Aprilu na shekara ta 2005, manyan limaman sun zabi Kardinal Joseph Ratzinger, kwanaki ukku ne bayan da ya cika shekaru 78 da haihuwa. Ko da shike a wannan lokaci, an ga kamar Paparoman yana da yarantaka tare dashi, amma shekaru takwas kan wannan kujera nan da nan aka ga yadda zurfin shekarunsa suka zama cikas a aiyukansa na yau da kullum. A bayan kula da shekaru, abin tambaya shine, ko rukunin Italiyawa 28 tsakanin Kardina-Kardinal dake zaben Paparoman, zasu hada kai da takwarorinsu yan Spain da Faransawa suma masu ra'ayin yan mazan jiya, domin zaben dan Italiya a matsayin sabon Paparoma, ko kuwa kamar a shekara ta 1978, da aka zabi dan Poland Karol Wotyla da kuma shekara ta 2005 da aka zabi Bajamushe Joseph Ratzinger, a wannan karoma za'a zabi wani ne daga waje? Shin za'a sake samun Paparoma ne daga Turai, ko a wannan karo zai fito ne daga nahiyar Afirka ko daga Latinamerika ko daga yankin Asiya. Idan kuma aka duba tsarin yadda manyan limaman yake, za'a ga cewar yana da wuya a zabi wani daga yankin Amirka. Duk da hakan, mutumin dake kan gaba cikin wadanda ake ambata sunayen su a matsayin masu gadon Paparoma Benedikt na 16 shine Kardinal Peter Turkson shugaban sashen zaman lafiya da daidaituwa a fadar Paparoma ta Vatikan.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal