Wallafe-wallfe kan sanin tushe | Himma dai Matasa | DW | 25.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Wallafe-wallfe kan sanin tushe

Wani matashi a kasar Afirka ta Kudu duka wajen rubuce rubucensa kan batutuwa da suka shafi auren jinsi guda, wanda aka yi yakinin ayyukansa na habaka kyakkyawar dangantaka.

Sonwabiso Ngacowa ya girma a wata anguwa da ke kusa da birnin Cape Town na kasar Afrika Ta Kudu. Baya ga alfahari da al'adarsa, yana kuma kula da cudanya da ka iya kawo kyakkyawar fahimta da aminci a tsakanin al'umma. To sai dai duk da wannan fafutuka, ba kowa ne ke yadda da alkiblar sa ba, ganin yadda kunnuwarsa ke ji masa suka da yake sha a cikin gari.

" Ba daidai bane nuna rashin da'a ga al'adata, ko da yake al'adar Zoha bai amince da tarayyan jinsi guda a matsayin ma'auta ba. To amma na fahimci cewa irin wadannan al'adu ba'a canza su, kuma yana da kyau a martaba yadda mutane suke rayuwarsu ta yau da kullum."

Sonwabiso dai, ya yi nazarin rayuwar matasan da aka haifa bayan girke tsarin demokradiyar Afrika ta kudu, a cikin wani sabon littafin da ya wallafa mai suna "21-21 the coming of Age of a Nation". Aikin dai ya ta'allaka ne ga 'yan sa'o'i guda da suka zo duniya a zamanin kawo karshen mulkin wariyar jinsi a shekara ta 1994.

Melanie Verwoed wani mai fafutuka ya dafawa Sonwabiso wajen jin ra'ayin yadda wadannan masu shekaru 21 ke kallon rayuwar yanzu a Afrika ta kudu, idan aka kwatanta da zamanin mulkin turawa.

Ita ma Yonela Tayatkeka wata matashiya ce, da ke wakar hip hop, na cikin wadanda suka bayyana ra'ayinsu, musamman na gamsuwar rayuwa a matsayin 'yar madigo, kamar yadda take cewa a wakarta na hip-hop.

Ko da yake dai, ko bayan shafe shekaru 21 da girke demokradiya a Afrika ta kudu, to amma har yanzu jahilci da tashe-tashen hankula na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a wasu yankunan kasar. A yanzu dai Sonwabiso da Yonela na ci gaba da gwagwarmayan samun sauyi, ta tsigar kalamansu a irin wallafe-wallafe da wake-wake da suke yi.

Sauti da bidiyo akan labarin