1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Botswana: Kokarin alkinta muhalli

Stefan Möhl Sp: Alhassan, Rabiu/A, AH, LMJ
December 10, 2019

Kasar Botsawana ta bunkasa harkar yawon bude ido da sababbin dabarun amfani da makamashi da aka sabunta domin magance matsalar sauyin yanayi da namun jeji.

https://p.dw.com/p/3UXmy
eco@africa Botswana's Green Safaris
Gandun dajin Botswana da masu yawon bude ido ke tururuwaHoto: DW

 

Kasar mai yawan mutane miliyan biyu, na karfafa gwiwar amfani da motocin da ke aiki da lantarki da hasken rana wato sola a karon farko a wurin shakatawarta na Chobe Game Lodge. Shugaban wurin shakatar John Bruer ya ce matakin zai tafi daidai da tsarin. Duk da cewa kasar Botswana na samun kaso biyar ne kacal na kudaden shiga daga harkar yawon bude ido, amma harkar ta samar da ayyuka dubu 70 ga 'yan kasar, kuma ita ce ta biyu mafi tasiri baya ga hako ma'adinin zinare.

A kasashen Afirka, farauta da karuwar yawan jama'a na tilasta namun daji kauracewa wuraren zamansu na asali. A shekarar 2012, kogin Chobe da babban wurin shakatawa da yawon bude idon sun zama cibiya mafi girma ta adana namun daji a Afirka. Bayan tsarin na sufurin motoci marasa fitar da hayaki da ke amfani da hasken rana, wurin shakatawar ya tanadi otal da ke aiki da tsarin makamashin da aka sabunta ga baki masu yawon bude idon.