Wa′adin mulkin Barak Obama na biyu ya fara. | Labarai | DW | 21.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wa'adin mulkin Barak Obama na biyu ya fara.

An rantsar da shugaban Amurika, a saban wa'adin mulki na shekaru huɗu.

Jiya ne a fadar White House aka shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki, domin rantsar da shugaba Barack Obama a wa'adin mulkin na biyu.Kamar yadda kudin tsarin mulkin Amurika ya tanada 20 ga watan Janiru ta kamata shugaban yayi rantsuwar kama aiki, to saida a wannan karo ranar ta faɗa Lahadi,wadda ke matsayin ranar hutu.Nan gaba a yau za a shirya wani gagaramin biki a birnin Washington, wanda ake sa ran kimanin mutane miliyan ɗaya za su halarta domin rantsar da shugaba Barack Obama.

A jawabin da zai gabatar albarkacin bikin, Obama zai baiyana mahimman bururukan da ya sa gaba a tsawan shekaru huɗu masu zuwa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal