Wa′adin ajiye makamai ga ′yan tawayen Seleka | Labarai | DW | 01.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wa'adin ajiye makamai ga 'yan tawayen Seleka

Gaza kwance damarar 'yan tawayen Seleka a Jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya na neman jefa yankin cikin rigima.

Makonni biyu bayan da shugaba Michel Djotodia na Jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya ya bayar da umarnin rushe kungiyar 'yan tawayen Seleka, wadda ya jagoranta, kana ta taka rawa wajen darewarsa bisa kujerar mulki watanni shidan da suka gabata, har yanzu 'yan tawayen na kin bin umarnin tsohon shugabnan na su wajen ajiye makaman. A yayin da kasar ke fama da tashe tashen hankula da kuma rashin bin doka da oda dai, yankin baki daya na fuskantar hatsarin shiga cikin rigingimu.

A cewar, janar Jean Felix Akaga, kwamandan dakaru 2,000 da kasashen yankin suka samar domin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya, rashin mutunta umarnin, na zama kaddamar da yaki ne a kan sauran kasashen yankin guda 10 da kungiyar ta Seleka ke yi. Ya kara da cewar, a yanzu rundunar ta yanke shawarar bai wa kungiyar ta Seleka wa'adin mako daya, wanda idan ba ta ajiye makamanta ba, to, kuwa dakarunsa za su yi amfani da karfin bindiga wajen tabbatar da ganin cewar sun yi hakan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe