Wa zai maye gurbin Paparoma?
February 12, 2013Sannu a hankali dai hankali na karkata daga gabar tekun Mexico ya zuwa ga ita kanta Turai da ma kudancin Amurka da nufin neman magaji ga Paparoman wanda babu zato ba tsammani ya ce ya gaji kuma jikinsa na bukatar hutu.
To sai dai ita ma nahiyar Afirka ba a bar ta a baya ba a kokarin samar da shugabancin da ke zaman mafi girma da daukaka a tsakanin mabiya darikar Katholika sama da miliyan dubu daya a sassa daban daban na duniya.
Paparoma daga Afirka
Akalla mutane uku da suka hada da Kardinal Francis Arinze da Kardinal John Oniyekan sannan kuma da Kardinal Olabunmi Okogie ne dai yanzu haka ke iya hawa kujerar daga Najeriya kasar dake da mabiya miliyan kusan 20 banda kuma Kardinal Peter Turkson wani dan kasar Ghana da dukkaninsu ke iya zama Paparoma kowane lokaci a cikin watan Maris mai zuwa.
Ana dai kallon zabar daya daga cikin hudun a matsayin kafa tarihin samar da baki na farko da zai shugabanci darikar mai tarihin kimanin shekaru dubu biyu.
Abun da kuma a cewar Reverend Father Zakaria Samjumi dake zaman daya daga cikin manyan jami'an kungiyar mabiya darikar a Najerya zai zamo abun farin ciki a garesu.
Wanene Francis Arinze
To sai dai koma wace ce hanya mafi bulla ga masu zaben sarki a cikin Vatikan din dai ya zuwa yanzu suna ambato Peter Turkson dan shekaru 64 kuma dan kasar Ghana da kuma Kardinal Francis Arinze dan shekaru 80 kuma dan Najeriyar da yayi suna a cikin fadar ta VatiKan a matsayin na kan gaba daga Afrika to sai dai shin wane ne Francis Arinze?
Reverend Father Ralph Madu dai na zaman sakataren kungiyar mabiya darikar Katholika a Najeriya mutumin kuma da ya fito daga karkara guda da Arinzen.
“Na san Kardinal Arinze a matsayin mai wa'azi da kuma mai kula da makarantar wa'azi. Kuma na sanshi da dadewa na je ma bikin cika shekarunsa 80 a garin Onitsha. Mutum ne mai yawan addu'a kuma mai ilimi yayi aiki na shekaru da dama a Vatikan, saboda haka ya san diplomasiyar da aikin coci ba kawai a matsayinsa na shugaban hukumar hadin kan addinai ba har ma a matsayinsa na shugaban hukumar tabbatar da bauta da biyayya.”
Duk da cewar dai bullar daya daga cikin biyun ba zai zamo Paparoma na farko daga nahiyar ta Afirka ba, dukkanin ragowar Paparoma ukun da suka fito daga nahiyar dai fararen fata ne kuma Romawa ga cocin da yanzu haka ruhin ta ke zaman dagewa irin ta mabiyan nahiyar.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal