Victor Ponta ya koma kan matsayinsa na Fraministan Rumeniya | Labarai | DW | 18.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Victor Ponta ya koma kan matsayinsa na Fraministan Rumeniya

Kasar Rumeniya ta jima tana fama da rikicin siyasa sanadiyar rashin jittuwa tsakanin shugaba da fraministan kasar. Abun da ke jinyo fargaba daga Tarayyar Turai.

default

Victor Ponta

Shugaba Traian Basescu na Rumeniya, ya sake naɗa abokin hamayarsa Victor Ponta a matsayin sabon shugaban gwamnati, bayan da haɗin gwiwar jam'iyun masu goyon bayan Firaministan suka lashe zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar a makon da ya shuɗe.
Su dai shuwagabin guda biyu, na fuskantar saɓani tun bayan da Firaministan Victor Ponta ya gabatar da ƙudurin neman tsige shugaban ƙasar a wani matakin kaɗa ƙuri'ar da 'yan ƙasar suka yi a watan Yulin shekara bana.
Masu nazarin al'amuran ƙasar Rumeniyan, sun bayana cewar sake naɗa Firaminista Ponta ya kasance tilas ne ga shugaban ƙasar,inda rashin yin hakan, kan iya jefa Rumeniya cikin wani ruɗanin siyasa mai tattare da rashin tabbas a wannan ƙasa da ke zawarcin shiga ƙungiyar Tarayyar Turai.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi