1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa ya dauki sabon salo a Venezuwela

Zulaiha Abubakar MNA
March 4, 2019

Tawagar 'yan adawa a kasar Venezuwela sun shirya tsaf don fantsama kan titunan kasar biyo bayan amsa kiran jigoran adawa Juan Guaido gabanin dawowarsa kasar daga zagayen neman goyon bayan shugabannin kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3EPnn
Venezuela Krise - USA schicken weitere Hilfsgüter - Juan Guaido
Hoto: Reuters/M. Quintero

Sake bullar Juan Guaido a kasar ta Venezuwela na iya zama barazana ga shugaba Nicolas Maduro wanda ke da zabin kame ko kuma haramta wa jagoran adawa fita daga kasar, lamarin da ka iya haifar wa Maduro Allah wadai daga kasashen ketare. Amma kau da kai ga aikin yada manufofin da Guaido ke yi a fadin kasar ke nuna alamun gazawar Maduro a matsayinsa na shugaban kasa.

Tun da fari jagoran adawar ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar gwamnatin Maduro za ta yi da na sani matukar ta yi gangancin kame shi ko magoya bayansa.

A makon da ya gabata ne dai Maduro wanda rundunar sojojin kasar ke mara wa baya ya gargadi jagoran adawar da kakkausar murya kan kiyayi fushin hukuma idan har ya sake shiga kasar ta Venezuwela.

Kasar dai ta shiga rudanin siyasa bayan da kasashen ketare suka goyi bayan Juan Guaido a matsayin shugaban rikon kwarya ko da yake kasashen Rasha da Chaina sun dauki alwashin kare martabar shugaba Maduro.