Maduro zai rufe iyakarsa da sauran kasashe
February 21, 2019Talla
Matakin gwamnatin na Venezuela na zuwa ne a dai dai lokacin da madugun adawar kasar da ke ikirarin shugabanci Juan Guido ya je kan iyakar kasar da Kwalambiya tare da wasu lauyoyi 80 domin duba yiwuwar shigo da kayan agaji da kasar Amirka ta aiko.
Jagoran adawa Guido tare da kasashen da ke mara masa baya na zargin Shugaba Maduro da jefa al'ummar kasar cikin yunwa da talauci sakamakon matsin tattalin arziki da kasar ke ciki.
Sai dai Shugaba Maduro da ke samun goyon bayan kasashen Rasha da China, ya zargi Amirka da neman yi wa gwamnatinsa zagon kasa tare da yi wa dimukuradiyya karan tsaye.