1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maduro na samun goyon bayan sojoji

Zulaiha Abubakar
February 20, 2019

Ministan tsaron kasar Venezuela Vladimir Padrino ya jaddada goyon sojojin kasar ga shugaba Nicolas Maduro bayan sanarwar shirin ko ta kwanan da dakarun da ke aikin tsaron kan iyakokin kasar suka yi.

https://p.dw.com/p/3Dhml
Venezuela Caracas neuer Verteidigungsminister Vladimir Padrino Lopez
Hoto: Getty Images/AFP/L. Robayo

Tun da fari ya bayyana cewar shugaban kasa daya suka sani kuma shi ne Maduro kuma ba  zasu amince da gwamnatin jeka nayi ka ba ko karbar umarni daga kasashen ketare sai dai a bayan ransu. Wannan jawabi na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump na Amirka ya gargadi Sojojin na Venezuela  kan ci gaba da goyon bayan gwamnatin Maduro. Jagoran adawar dai wanda da dama daga cikin kasashen Turai ke marawa baya, ya umarci al'ummar kasar su ci gaba da zanga-zanga.