1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guaido: Kisan mummuke a Venezuela

Lateefa Mustapha Ja'afar ATB
February 12, 2019

Jagoran adawa a kasar Venezuela da ya ayyana kansa a masatyin shugaban kasar na riko Juan Guiado ya bukaci sojojin kasar da su kawo karshen rufe kan iyakoki domin bayar da damar shigar da kayan agaji.

https://p.dw.com/p/3DDtQ
Venezuela | Juan Guaido
Hoto: Reuters/C. Garcia Rowlins

Tun bayan da Juan Guaido ya ayyana kansa a matsyin shugaban riko, kasar Venezuela ta kara tsunduma cikin rikici da kuma halin rashin tabbas, sakamakon goyon bayan da Guiado ya samu daga kasashen ketare musamman Amirka da kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU.

Baya ga fargabar tashin hankali akwai matsaloli da suka danganci rashin kayan agaji, abin da ya jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin hali na rashin abinci da magunguna da kuma sauran kayan masarufi, sakamakon rashin shigowar kayan agaji cikin kasar. A hirarsa da tashar DW, jagoran adawar Juan Guaido ya bukaci sojojin kasar su yi watsi da Shugaba Nicolas Maduro su kuma taimaki al'ummar da ke cikin halin tasku ta hanyar bude kan iyakar domin shigo da kayan agajin.

 

Venezuela Kolumbien Grenzübergang bei Cucuta
Hoto: DW/F. Abondano

"Kullum muna yin kira ga sojojin kasar da su yi amfani da dokokin da kundin tsarin mulki ya tanadar. Mun bayyana musu karara cewa tilas su bari a shigar da kayan agaji, mun kuma shaida musu cewa duk wanda ya hana, zai gurfana gaban kuliya bisa zargin take hakkin dan Adam."

Sai dai kiran na Guiado bai samu karbuwa daga sojojin ba, maimakon haka sun kaddamar da sabon atisaye na nuna goyon baya ga Maduro wanda ya ki barin shigar da kayan agajin cikin kasar, yana mai cewa zai kasance mafarin mamaye kasar da Amirka za ta yi.

"Dubban sojojinmu maza da mata sun nuna bajintarsu da horonsu da karfin zuciya da jajircewarsu. Karfin da za mu nuna wa kasashen ketare su fice daga kasarmu. Al'ummar Venezuela mu daga hannuwanmu, ku fice daga kasarmu 'yan daular yankee masu cika baki a waje su kuma yi mulkin kama-karya a gida."

Sai dai cikin hirar tasa da DW Guaido ya nunar da cewa matakin sojojin bai karya masa gwiwa ba, domin a cewarsa har yanzu yana da yakinin cewa zai iya shawo kansu su amince a shigo da kayan agajin cikin kasar. Koda yake ya ci gaba da barazanar daukar tsauraran matakai a kan mutanen da ya kira da masu take hakkin dan Adam.