1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela: 'Yan juyin mulki a ko ina

Jan D. Walter/ LMJMay 19, 2016

Shugaba Nicolas Maduro ya samu wani iko na musamman don dakile barazanar juyin mulki. Sai dai 'yan adawa na amfani da halastattun hanyoyi.

https://p.dw.com/p/1IqhA
Caracas Proteste Polizei Demonstranten auf Straße
Hoto: Getty Images/AFP/F.Parra

Masu zanga-zanga a Venezuela na neman da a kada kuri'ar raba gardama da za ta bayar da damar sauke shugaban kasar Nicolas Maduro. A ranar Laraba dai masu zanga-zangar sun fito kan tutuna domin nuna adawarsu da gwamnatin ta Venezuela duk kuwa da kokarin tarwatsa su da jami'an tsaro suka yi ta hanyar watsa musu hayaki mai sa hawaye da kuma dokar ta bacin da aka sanya a kasar. Shi ma dai Shugaba Nicolas Maduro ya yi gargadi ga masu zanga-zangar adawar da kada su mayar da ita tarzoma in kuwa ba haka zai dauki matakin ba sani ba sabo a kansu. Shugaban dai ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dawo da doka da oda a kasar in har masu zanga-zangar suka nemi tayar da zaune tsaye.

Halin rashin tabbas a kasa

'Yan adawar kasar ne dai suka shirya wannan zanga-zanga a Caracas babban birnin kasar da ma sauran manyan birane da garuruwa, domin yin matsin lamba na ganin an gudanar da kuri'ar raba gardama da za ta bayar da damar hambarar da Shugaba Maduro daga kan karagar mulki cikin wannan shekara.

Nicolas Maduro
Shugaba Nicolas Maduro na VenezuelaHoto: Getty Images/AFP/A.Burton

'Yan adawar dai na zargin Maduro da sanya kasar cikin halin tasku na tsaka mai wuya da ma batun sanya dokar ta baci domin hana su yin zanga-zangar adawa da shi, inda suka bukaci majalisar dokokin kasar da ta kada kuri'ar sauke shi daga kan karagar mulkin. A wani jawabi da ya yi, Maduro ya bayyana cewa.

"Ba haka ba ne, majalisa na son ta sauke ni, in har suka hana ni ko wane irin motsi kana ban sanya dokar ta baci ba, ba za mu iya zartas da ko wane irin kudiri ba. Misali karin kudin fansho da na albashi da batun kasafin kudi, kasancewar komai sai ya bi ta hannun majalisun dokoki, za su iya kin amincewa da shi domin kawai su yi wa gwamnati kafar ungulu tare da wargaza yanayin tattalin arzikin da muke ciki."

Ta hanyoyi biyu ne dai za a iya sauke Shugaba Maduro a kasar, inma majalisar dokokin kasar ta yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta hanyar rage wa'adin shugabanci na shugaban kasa daga shekaru shida zuwa hudu ta yadda za a gudanar da sabon zaben shugaban kasa a karshen wannan shekara ta 2016, ko kuma ta hanyar kada kuri'ar raba gardama, hanyar da 'yan adawar kasar ke son bi a yanzu. Sai dai tuni gwamnati ta yi watsi da batun kada kuri'ar raba gardamar tare da kara wa Shugaba Maduro karfin iko.

Dole 'yan adawa sun yi a sannu

Enrique Capriles Venezuela Caracas
Enrique Capriles jagoran 'yan adawaHoto: picture-alliance/dpa/M.Gutierrez

Duk da wannan mataki na da jam'iyyar adawa ta Democratic Unity Roundtable MUD a takaice ta dauka na ganin an kifar da gwamnatin Maduro, kwararru na ganin cewa tilas ne sai sun yi takatsantsan, ganin cewa yana da goyon bayan sojojin kasar kana al'ummar kasar da dama na mara masa baya. Claudia Zilla, shugabar cibiyar bincike kan kimiyyar siyasa ta Amirka da ke birnin Berlin na kasar Jamus ta nunar da cewa akwai aiki a gaban 'yan adawar kasar.

"Kawo yanzu za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, sun zama tsintsiya madaurinki daya, sai dai in dunkulewar ta su ta zamo tarwatsewa, sojoji za su dauki mataki a kansu, ba lallai ne su samu abin da suke bukata ba."

Gwamnatin dai ta kara wa'adin dokar ta baci kan tattalin arzikin kasar zuwa wasu shekaru 60, abin kuma da 'yan adawar ke zargin Shugaba Maduro da kokarin hana kasar ci gaba. Sai dai kan wannan batu ma Maduro cewa ya yi:

"Na dogara ne a kan sakin layin da ke karkashin doka ta 338, zan iya kara wa'adin doka ko kuma kirkirar doka kan yanayin tattalin arziki. A yanayin da muke ciki yanzu ta yadda shugaban Amirka Barack Hussein Obama ke yin barazana ga kasarmu da ma barazanar da tsohon shugaban kasar Columbiya Alvaro Uribe ya yi na cewa ya kamata a kai wa Venezuela harin sojoji tare da mamayeta, ya kamata mu yi takatsantsan."

Tuni dai sama da mutane miliyan guda suka sanya hannu kan wata takaddar neman kada kuri'ar raba gardamar tare da mika ta ga hukumar zaben kasar CNE a makwanni biyun da suka gabata.