1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela ta yanke hulda da Amirka

Ahmed Salisu RGB
January 25, 2019

Jami'an ofishin jakadancin Amirka sun fice daga Venezuela bayan da shugaban kasar ya sanar da yanke huldar jakadanci da Amirka biyo matakin shugaba Trump na amince da madugun adawa a matsayin shugaban kasa na riko.

https://p.dw.com/p/3CDT8
Venezuela Nicolas Maduro in Caracas
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Cubillos

 A wannan Juma'ar ce jami'an na diflomasiyyar Amirka suka fara ficewa daga Venezuela din bayan da sakataren harkokin wajen Amirka, Mike Pompeo ya umarci wasu daga cikinsu da su fice daga kasar biyo bayan lalacewar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Gabannin ficewarsu dai, madugun 'yan adawar kasar Juan Guaido da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya ya nemi jami'an diflomasiyyar Amirka din dasu cigaba da zama a kasar sai dai ga alama wannan haka tasa ba ta cimma ruwa ba.

A daura da wannan batu, kasashen duniya ciki kuwa har da Spain na cigaba da daukar matsayi kan rikicin siyasar Venezuela din. Ta baya-bayan nan dai ita ce Jamus wadda ta ce lokaci ya yi da Maduro zai yi bankwana da gadon mulki kasancewar zaben da aka yi wanda ya dora kan mulki kasar ba shi da sahihanci.

Ita kuwa Rasha cewa ta yi ba ta amince da jingine Maduro a matsayin shugaban Venezuela ba. Jakadan Rasha a zauren Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia ya ce Moscow ba ta goyi bayan duk wani shiri na sauya shugabanci a Venezuela ba ciki kuwa har da kudurin da Amirka za ta gabatar a Majalisar ta Dinkin Duniya kan amincewa da Guaido a matsayin shugaba na riko.

Bayan ga matsayin da Rasha ta dauka na kin juya baya ga Maduro, wasu rahotanni daga kasar na cewar jami'an tsaro da suka kware wajen kare lafiyar mutum, sun isa Venezuela din domin dafawa dogaran shugaban wajen tsaron lafiyarsa a fadarsa da ke Caracas babban birnin kasar.