1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shirya gudanar da gagarumin gangamin korar shugaba Maduro

Ramatu Garba Baba
February 2, 2019

Kallo ya koma sama a tsakanin Shugaba Nicolas Maduro da jagoran adawa Juan Guaido da ya kira wani gagarumin gangami don tilastawa Maduro yin murabus daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/3CbVr
Venezuela Anti-Regierungs- Proteste in Caracas
Hoto: Getty Images/AFP/F. Parra

Guaido da ke samun goyon bayan manyan kasashen duniya, ya yi facali da duk wani tayi na shiga yarjejeniya da Shugaba Maduro ya yi masa,  inda ya kafe kan a gudanar da sabon zabe bisa tafarki irin na demokradiyya. Madugun adawan ya ce lokaci ya yi da Venezuela za ta fita daga cikin yanayi da gwamnati mai ci ta jefa jama'ar kasa, na rayuwa cikin kunci da yunwa da talauci da tauye hakkin dan adam. Rikicin siyasa ya barke makonni biyu da suka gabata bayan da Juan Guaido ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko.