Dan kishin kasa ya mika wuya a Ostiriya
December 4, 2016Talla
Zaben shugaban kasar Ostiriya ta tabbata dan taka na jam'iyyar kare muhalli Alexander Van der Bellen ya samu nasara da kusan kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada a wannan Lahadi, yayin da mai ra'ayin rikau Norbert Hofer ya rungumi kaddara. Rufe tashoshin zabe ke da wuya aka fara sanin wanda zai lashe zaben tsakanin mutanen biyu.
Shi dai Alexander Van der Bellen wanda ya lashe zaben ya kasance mai goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai, yayin da Norbert Hofer ya nuna kansa a matsayin dan kishin kasa wanda zai kare kasar ta Ostiriya daga bakin haure da ke kwakwara suka gurbata al'adun da aka saba da su a kasar.
Sai zuwa goba Litinin kafuin samun cikekken sakamakon zaben a hukumance bayan kirga kuri'un 'yan kasar mazauna kasashen ketere.