Usain Bolt ya kare kambunsa a tseren mita 100 | Labarai | DW | 23.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Usain Bolt ya kare kambunsa a tseren mita 100

Usain Bolt ya yi nasara a kan babban abokin hamayyarsa dan kasar Amirka Justin Gatlin da dakika daya bayan da ya yi gudun mita 100 a cikin dakikoki 9.79 a gasar wasannin motsa jiki ta duniya a Bejing.

Shahararren dan tseren kafar nan dan kasar Jamaika Usain Bolt ya yi nasarar kare kambunsa a gudun fanfalakin mita 100 a gasar wasannin motsa jiki ta duniya da ke gudana yanzu haka a birnin Bejing na kasar Chaina. Usain Bolt ya yi nasara a kan babban abokin hamayyarsa dan kasar Amirka Justin Gatlin da dakika 0.01, bayan da ya yi gudun mitan 100 a cikin dakikoki 9.79 a yayin da abokin hamaiyar tasa ya kai da dakika 9.80.

Wannan nasara ta bai wa zakaran duniyar dan kasar Jamaikar dan shekaru 29 damar zamowa gagarabadau a fagen gudun kafar na mita 100 inda a jimilce ya samu tammayen zinare 11 da matsayin zakaran duniya sau tara tun bayan assasa gasar wasannin motsa jiki ta duniya a shekara ta 1983.

A ranar Talata mai zuwa Usain Bolt din da abokin hamayyar tasa dan kasar Amirka za su sake fafatawa a gudun tseren mita 200.