UNICEF :Yara na mutuwa a Tekun Mediterranean | Labarai | DW | 14.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UNICEF :Yara na mutuwa a Tekun Mediterranean

Asusun yara kanana na MDD ya ce yara tara bisa goma da aka yi hijira da su a wannan shekara zuwa Turai ta Italiya sun zo ne ba tare da 'yan rakiya ba.

A cikin wani rahoton da asusun ya bayyana wanda aka yi wa la'akabi da sunan hadari a kowane taki. ya ce yara kanana kimanin dubu bakwai wadanda ba su tare da rakiya sun tsallaka tekun Mediterranean daga yankin Arewacin Afirka zuwa Italiya a cikin watannin biyar na farkon wanman shekara.

Kuma tun farkon watan Janeru kawo yanzu sama da mutane dubu biyu da dari takwas suka mutu a cikin tekun na Mediterranean mafi yawancinsu yara kanana.