UNICEF: Yara miliyan 50 ke yin hijira a duniya | Labarai | DW | 07.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UNICEF: Yara miliyan 50 ke yin hijira a duniya

Asusun kula da yara kanana na MDD UNICEF ya ce kusan yara miliyan 50 suke barin kasashensu na asli domin yin hijira a cikin wasu kasashe saboda dalilian yake-yake, da kuma wasu matsalolin da kan tasowa.

Asusun ya ce a shekara ta 2015 da ta wuce kimanin kishi 45 cikin dari na yaran 'yan gudun hijira da ke a karkashin kulawar MDD 'yan asilin kasashen Siriya ne da Afganistan wadanda yaki ya sa suka baro kasashensu.

Mataimakin daraktan asusun ya ce akwai bukatar a daina raba yara da iyayensu akasari 'yan ci rani masu neman mafaka.