Umurnin kama firaministan Pakistan | Labarai | DW | 15.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Umurnin kama firaministan Pakistan

Kotun kolin Pakistan ta bayar da umurnin cafke firamistan kasar Raja Ashraf da kuma wasu fitattun 'yan siyasa 15 bisa zargin cin hanci da karbar rashawa.

Kotun kolin Pakistan ta bayar da umurmin cafke firaministan kasar Raja Pervez Ashraf wanda ake zargi da laifin cin hanci da kuma karbar rashawa. Daya daga cikin lauyoyin gwamnati da ya bayar da sanarwar a birnin Islamabad, ya kuma ce kotun ta bayar da sammacen kame karin fitattun 'yan siyasa 15 bisa makamanci laifin na karbar toshiyar baki. Ana dai zargin su da marar hannu a badakalar bayar da wasu jerin kwangilolin a fannin makamashi ba bisa ka'ida ba.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati Ali Zardari ke fuskantar kalubale watannin kalilan kafin gudanar da zaben gama gari a farkon watan mayu. Wani malamin dan kasar mai takardun Canada, Tahir Qadri ya shirya gagarumar zanga zangar ta kwanaki biyu , domin tilasta wa gwamnati yin murabus tare da rusa majalisar dokoki saboda gaza magance matsalar cin hanci dakarbar rashawa da ta yi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu