Daga Senegal Embalo ya isa Brazzaville,
November 29, 2025
Talla
A ranar Laraba, sojoji suka hambarar da gwamnatin Embalo tare da dakatar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu na ranar 23 ga Nuwamba.
An tsare Embalo na ɗan lokaci a hannun sojoji , kafin su barshi ya tafi Senegal, a cikin jirgin da gwamnatin a yi hayarsa.
A yanzu ya isa Brazzaville don zama a cewar wata majiya da ke kusa da fadar shugaban ƙasar Kwangon.