1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta zargi Rasha da takalar fada

April 12, 2014

Ukraine ta bukaci Rasha da ta daina daukar matakan da ta bayyana da takalar fada biyo bayan kwace iko da ginin gwamnati da tsageru masu goyon Rasha su ka yi.

https://p.dw.com/p/1BgzX
Hoto: picture-alliance/dpa

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Ukraine din ce ta bukaci hakana dai dai lokacin da tsageru masu goyon bayan Rashan ke ci gaba da kwace gine-ginen ofisoshi da hukumomin gwamnati a yankin Slaviansk na gabashin Ukraine din. Mai rikon mukamin ministan harkokin kasashen ketare a gwamnatin rikon kwaryar Ukraine din Andrii Deshchytsia ne ya bayyana hakan inda ya ce ya tattuana ta wayar tarho da ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Sergei Lavrov kan batun. Rasha dai ta musanta bada ko wane irin taimako ga tsagerun dake rike da makamai wanda a zahiri matakan tsagerun ke da nasaba da zabar komawa karkashin ikon Rashar da yankin Kirimiya na Ukraine din ya yi.

Tun da fari dai Firaministan rikon kwarya na Ukraine din Arseniy Yatsenyuk ya kai wata ziyarar bazata yankin Donetsk dake da arzikin ma'adinai da shima yake kokarin ballewa ya koma karkashin ikon Rasha. Yatsenyuk ya gana da mahukuntan yankin inda ya yi gargadi ga tsagerun da su fice daga guraren da suka mamaye tun kafin gwamnati ta dauki matakan yin amfani da karfi a kansu. Tsagerun yankin na Donetsk sun kwace iko da mafiya yawa daga cikin ofisoshi da hukumomin gwamnati a yankin inda suke yin kira ga al'ummar yankin kan su kada kuri'ar raba gardama domin suma subi sahun takwarorinsu na yankin Kirimiya wajen komawa karkashin ikon Moscow batun da kasashen yamma ke yin adawa da shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar