Ukraine na tunawa da fara boren Maidan | Labarai | DW | 21.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine na tunawa da fara boren Maidan

Shugaban Ukraine da mataimakin shugaban Amirka sun halarci biki a wannan dandali tare da karrama waɗanda rikicin da ƙasar ke fama da shi ya lamshe rayukansu.

Shugaban Ukraine Petro Poroschenko ya jagoranci bikin tunawa da zanga-zangar neman sauyi da ta ɓarke a dandalin Maidan na birnin Kiev shekara guda ke nan cif da ta gabata. Shugaban ya yi amfani da furrani wajen karrama mutane kimainin 100 da rikicin da ya biyo bayan ya lamshe rayukansu.

Firaministan ƙasar ta Ukraine da kuma mataimakin shugaban Amirka Joe Biden na daga ckin waɗanda suka halarci wannan biki. A ranar 21 ga watan Nowamban bara ne dai duban 'yan Ukraine suka fara tayar da kayar baya don nuna adawa da matakin da shugaban wannan lokaci ya ɗauka na kulla kawance da Rasha maimakon ƙungiyar gamayar Turai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane