Ukraine na neman sake tattaunwa da ′yan tawaye | Labarai | DW | 04.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine na neman sake tattaunwa da 'yan tawaye

Shugaban Petro Poroshenko ya faɗawa kantomar da ke kula da harkokin wajen Turai, Catherin Ashton cewa a shirye yake ya ƙaddamar da sabuwar tattaunawa da 'yan tawayen a ƙarƙashin jangoranci EU.

A wata sanarwar da ofishin Poroshenkon ya fitar, ya ce ya riga ya bayar da lokaci da wajen da za su gana, yanzu amsa ka dai yake jira daga wajen 'yan awaren.

Sai dai a wani labarin kuma, ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce tana nuna adawa da yadda Rasha ta saɓawa dokokinta na sufurin sama, kuma ta buƙaci da ta dakatar da duk abin da take yi cikin gaggawa. Ma'aikatar ta ce jirage masu saukar ungulu guda uku da ke ɗauke da tambarin Rasha ne suka karya waɗannan dokoki sau da yawa kuma ta sanar da Rashar fushinta a cikin wata wasiƙa da ta tura mata.

Mawallafiya : Pinado Abdu
Edita : Abdourahamane Hassane