Uhuru Kenyatta zai gurfana agaban kotu | Labarai | DW | 21.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Uhuru Kenyatta zai gurfana agaban kotu

Duk da lashe zaben shugaban kasar Kenya da Uhuru Kenyatta ya yi, yayin babban zaben kasar da ya gudana, Kotun ICC ta ce zai gurfana gabanta a watan Nuwamba.

Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC, ta dage lokacin da za ta saurari karar sabon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, daga ranar Talata mai zuwa har sai watan Nuwambar wannan shekara da muke ciki, inda ta ce ta dage sauraron karar ne domin ta baiwa lauyoyinsa damar kara yin nazari kan shaidun da aka gabatar mata.

Kenyatta na fuskantar tuhuma a kan laifuka guda biyar da suke da nsaba da cin zarafin dan Adam, da suka hadar da kisan gilla da fyade da kuma rawar da ya taka yayin rikicin bayan zaben shekara ta 2007 da akayi a kasar ta Kenya, da ya haddasa asarar rayuka masu yawa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe