UEFA ta buƙaci a ɗage zaman taron FIFA | Labarai | DW | 28.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

UEFA ta buƙaci a ɗage zaman taron FIFA

A kwai almun cewar za a samu ruɗani a taron na yau da FIFA ta shirya gudanarwa bayan kame wasu jami'anta.

Ƙungiyar wasannin ƙwallon kafa ta Duniya FIFA na shirin gudanar da taronta karo na 65 a yau a birin Zurich na Switzerland domin zaɓen sabbin shugabannin.

Duk kuwa da yadda aka cafke wasu mayan jami'an ƙungiyar guda bakwai da kuma wasu tsofi,waɗanda ake zargi da laifin yin zamba da cin hanci da kuma halita kuɗin haram a cikin shekaru 24. Waɗanda Amirka ta buƙaci a tusa mata ƙeyarsu domin su gurfana a gaban kotu.Sai dai a taron na yau na FIFA a kwai alamun cewar za a samu riginginmu saboda kuwa reshen ƙungiyar na wasannin ƙwallon kafa na Turai UEFA ya buƙaci a ɗage zaman.