Tushen rikicin siyasar da Amurka ke ciki | Siyasa | DW | 16.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tushen rikicin siyasar da Amurka ke ciki

Kwararru kan lamuran da ka je su zo, sun bayyana rikicin siyasar da ya ritsa da gwamnati, tamkar wani sabon yakin batsatsa ne tsakanin yankunan arewaci da kudancin Amurka.

A cewar masana kamar Editan mujallar nan da ke fita ta yanar gizo mai suna "The Globalist" watau Stephan Richter, wannan batun ya shige yadda ido yake hange.

"Idan muka yi la'akari da ainihin matsalar da ake fuskanta a yanzu, zamu ga cewar mutanen da ke adawa da shirin kiwon lafiya da aka yi wa lakabi da Obamacare, kuma ke neman hanyoyin da za su toshe amincewa da kasafin kudin Amurka, mutane ne da suka fito daga jihohin Amurkan da a baya can suka yi kaurin suna wajen gudanar da cinikin bayi".

A da jihohin yankin kudancin guda 11 ne. Kuma a yanzu haka akwai jihohi 10 dake nuna adawa da wannan shiri da ke taimakawa talakawa a fannin kiwon lafiya, wanda aka sha kai ruwa rana kafin kotun kolin Amurkan ta tabbatar da shi, in ji wannan Edita wanda kuma lauya ne da ya kasance a Amurka na tsawon shekaru 30 da suka gaba: "banda jihar Arkansas, manufar sauran sauran jihohin yankin kudancin Amurkan shine, ci gaba da yakin batsatsan kasar wanda ake zaton an kawo karshensa a shekara ta 1865".

Masana na ganin cewar lokaci yayi da za'a samu sauyin yanayi a Amurka. Musamman bisa ganin cewar marasa rinjaye daga cikin al'ummar kasar wadanda akasarinsu Amurkawa bakaken fata ne, da wasu dake da jinin yankin Asiya da kuma wadanda aka fi sani da latin Amurka, musamman sabbin yara da aka haifa, sune rabin yawan al'ummar Amurka.

A jihohin kudancin kasar dai, ana iya ganin yadda tsoffin Amurkawa fararen fata da suka rasa ayyukansu a masa'antu ke ganin an samu sauyi dangane da yadda tsarin kasar yake, wanda kuma basu shirya don hakan ba. A cewar Richter dai wannan tamkar muzantawa ce ga shugaban kasar kasancewarsa bakin fata.

Ra'ayin masani kan kimiyyar siyasa James Thurber, wanda ke zama direktan cibiyar nazarin ilimin shugabancin kasa da aikin majalisa a jami'ar Amurka da Washington,ya zo daidai da na Edita Richter. A cewarsa akwai 'yan asalin kudancin kasar masu matsanancin ra'ayin 'yan mazan jiya na demokrate, wadanda sakamakon canji da aka samu suka yi sauyin sheka zuwa jami'yyar Republican."Masu wannan ra'ayi daga kudancin Amurkan, suna adawa da gwamnatin tsakiya mai karfi, kazalika suna adawa da shirin kiwon lafiya na Obamacare".

U.S. House Speaker John Boehner (R-OH) speaks to the press following a House Republican party meeting on Capitol Hill in Washington, October 8, 2013. Boehner renewed his call on Tuesday for deficit-reduction talks with President Barack Obama and signalled that the discussions would be wide open. REUTERS/Jason Reed (UNITED STATES - Tags: POLITICS)

John Boehner

Masanin kimiyyar siyasar Amurkan ya kara da cewar, a yau muna ganin yadda yakin basasar da aka kawo karshensa shekaru masu yawa da suka gabata, yana taka muhimmiyar rawa, amma bangaren masu matsanancin ra'ayin 'yan mazan jiya.kusan 30 zuwa 40 daga cikinsu suke wannan fafutuka a majalisar Amurkan, wadanda ba masu tsattsauran ra'ayi bane.

Thurber yana mai ra'ayin cewar a wannan yanayi da ake ciki dai da kamar wuya a cimma wani daidaito tsakanin bangarorin biyu, saboda yadda majalisar Amurkan ta ke. Shekaru 30 baya dai, masu matsakaitan ra'ayi kashi 30 na 'yan majalisar. Wanda hakan ne ya ke basu daman fadin albarkacin baki, ko kuma kin amincewa da wani batu da basu yarda da shi ba. Amma a yanzu haka suna da kashi biyu ne kacal a majalisar, wanda ba zai basu damar yin katabus ba, balle wani tasiri. Haka ne kuma lamarin yake lokacin da yakin basasa ya barke a amurka a shekara ta 1860, lokacin da aka yi ta samun makamai daga mazabu daban daban.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal

Sauti da bidiyo akan labarin