1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Zango na biyu na shirin Tushen Afirka ga matasa

Mohammad Nasiru Awal
August 13, 2020

Wannan shirin DW mai suna "Tushen Afirka" na amfani da majigi da rahotannin rediyo wajen bayyana siffofin mashahuren mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka.

https://p.dw.com/p/3guhm
DW African Roots | Sheikh Usman dan Fodio

A zango na biyu na shirin DW kan "Tushen Afirka" ga matasan nahiyar kamar na farko ana amfani da majigi da rahotannin rediyo wajen bayyana shahararrun mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka.

Gidauniyar Gerda Henkel ce ta dauki nauyin shirin da aka kaddamar da zango na biyu a farkon watan Maris 2020 a birnin Legas na tarayyar Najeriya.

"Batutuwa kan tarihin Afirka na matukar daukar hankali a ayyukanmu," a cewar Claus Stäcker, shugaban sashen Afirka na DW wanda kuma ya assasa shirin zango na biyu a Legas.

Shirin na bayani dalla-dalla kan mutane maza da mata 'yan Afirka da tarihi ba zai taba mantawa da su ba.

Wani muhimmin abu a wannan karo shi ne akwai wani kwamitin mashawarta na 'yan Afirka masana kimiyya da ke duba kan dukkan rahotannin gabanin mu wallafa su.

Matasa da suka halarci bikin kaddamar da Tushen Afirka zango na biyu a Legas
Matasa da suka halarci bikin kaddamar da Tushen Afirka zango na biyu a LegasHoto: DW/C. Stäcker

Da ma dai ma'abota tashar DW sun nunar da cewar a mafi yawan lokuta ana ba da tarihin Afirka ne ta fuskar kasashen da suka yi musu mulkin mallaka. Wannan rata ce shirin "Tushen Afirka" ke neman cikewa. 

Sassan Afirka na DW sun dogara kan majiyoyi masu tushe daga Afirka, tare da hada gwiwa da masana tarihi, da al'adu da marubuta na Afirka don gudanar da aikin. Kuma ya fi raja'a kan matasan kasancewa sun fi kowa yawan a nahiyar.

Shirin "Tushen Afirka" zango na biyu zai rika zuwa muku ranar Alhamis da rana, sannan a maimata shi ranar Lahadi a shirin rana.