Turai za ta tura dakarunta Bangui | Labarai | DW | 20.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai za ta tura dakarunta Bangui

Turai ta ce ta yanke shawarar tura dakarunta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ne domin taimakawa wajen inganta ayyukan jinƙai

A yayin da Majalisar dokokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke ƙoƙarin zaɓen sabon shugaban ƙasa,

Ministocin kula da harkokin wajen Turai sun yanke shawarar tura dakarun Nahiyar zuwa ƙasar domin marawa dakarun Faransan dake wanzar da zaman lafiya a yankin.

Faransa wadda ta tura dakaru dubu ɗaya da ɗari shidda a watan da ya gabata na neman tallafi, kuma ministocin na ƙasashe 28 dake nahiyar sun ce ana buƙatar aƙalla dakaru 400 zuwa 600

Bisa bayyanan kamfanin dillancin Associated Press, Jami'an diplomasiyyan Turai suna buƙatan tura dakarun ne domin su mayar da hankali kan Bangui, da filin jirgin saman ƙasar, kana kuma su gudanar da sauran ayyukan jinƙan da ake buƙata a tsukin watanni shidda.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh