1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai da Amirka za su gyara kasuwancinsu

Yusuf Bala Nayaya
March 20, 2018

Sabon ministan tattalin arziki na Jamus Peter Altmaier ya bayyana kyakkyawan fata na cimma matsaya tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da Amirka kan batun haraji na karafa da farin karfe.

https://p.dw.com/p/2uc1i
USA Peter Altmaier, Wirtschaftsminister in Washington
Peter Altmaier sabon ministan tattalin arziki da kasuwanci na Jamus Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm

Altmaier ya bayyana wa manema labarai a gaban fadar White House cewa tattaunawarsu da jami'ai na Amirka ta ba da hasken cewa harkokin kasuwancinsu da Amirka a wannan fannoni ba za su tawaya ba. Ya kuma bayyana haka ne gabannin fara aiwatar da shirin kara harajin fiton karafa daga ranar Juma'a.

Altmaier ya ce za su dauki makonni suna sake nazari kan yarjejeniyar kafin a fitar da maslaha ta karshe. Kawayen Amirka dai ta fiskar kasuwanci da kungiyoyi na masu masana'antu da 'yan majalisa daga bangaren Republican da kasuwa an shiga tirka-tirka bisa fargabar shiga yanayi na yakar harkoki na kasuwanci a duniya bayan da Trump ya bayyana kari na kashi 25 kan karafa da kashi goma cikin dari kan farin karfen aluminium matakin da ya ce ya  dauka ne don kare muradun Amirka.