Tunisiya kasa ce ta arewacin Afirka da ke tsakanin LIbiya da Aljeriya. Ta samu 'yancin kanta daga Faransa a shekarar 1956.
Ta na da al'umma miliyan 11, kuma Tunis ne babban birninta. Shugabanta na farko Habib Bourguiba ya kafa dokar da ta baiwa mata cikakken 'yanci a kasar. A can ne guguwar neman sauyi ta kasashen Larabawa ta fara kadawa a shekara ta 2011.