Tsadar rayuwa a Tuniyasa
May 2, 2019Talla
Gwamnatin Tunis din dai na cigaba da fuskantar tirjiya daga bangaren al'umma da ke neman karin albashi, biyo bayan tsadar rayuwa da faduwar darajar kudin kasar, daura da matsin lamba na masu bayar da bashi na kasa da kasa, kan bukatar aiwatar da mataki na tsuke bakin aljihu.
A jiya Laraba ne dai, hukumomin kasar suka sanar da karin mafi kankantan albashin ma'aikatan masana'antu da gonaki, da ma masu karbar pansho da wajen kashi 6.5, wanda ke da nufin sassauta wahalar rayuwa.
Sai dai yajin aikin da ma'aikatan man fetur din suka kaddamar na bukatar karin a kalla dalar Amurka 100 a wata, shi ne na baya bayannan da ke haifar da tsaiko a harkokin ilimi da kiwon lafiya da ma bangaren sufuri.