Rikicin siyasa a Tunisiya
August 24, 2019Nabil Karoui mai shekaru 56 a duniya ya yi fice wajen sukar lamirin gwamnatin kasar ta wani gidan talabijin mai zaman kansa mallakinsa, tun bayan rasuwar shugaban kasar Beji Caid Essebsi a watan da ya gabata. A ranar juma'ar da ta gabata ne hukumar kula da sadarwa ta kasar da hadin gwiwar hukumar zabe a Tunisiyan suka dakatar da wasu manyan kafafen yada labarai daga aiki wadanda suka hadar da gidan talabijin na Nessma mallakar Karoui da ke zaman dan takarar shugabancin kasar .
An dai jiyo Karoui na bayyana tuhumar da ake masa da yarfe don a rage masa farin jini da karbuwa tsakanin al'ummar kasar. A ranar 15 ga watan Satumba mai kamawa za a gudanar da zaben shugaban kasa a Tunusiyan, bayan rasuwar tsohon shugaban kasar marigayi Beji Caid Essebsi wanda ya yi nasarar zama shugaban kasar na farko a tafarkin Dimukuradiyya.