Tunisiya ta shiga rudanin siyasa | Labarai | DW | 20.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tunisiya ta shiga rudanin siyasa

Rikicin siyasar Tunisiya ya kama hanyar kara rincabewa bayan da firaiminista Hamadi Jebali ya yi murabus.

A supporter of the Ennahda ruling party holds up a Koran as others shout slogans during a demonstration in Tunis February 16, 2013. Tens of thousands of supporters of Tunisia's Islamist-led government marched in the capital on Saturday, one of the biggest in a series of pro-government and opposition rallies sparked by the assassination of a secular politician. REUTERS/Anis Mili (TUNISIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS)

Tunesien Protest Demonstration Streik Islamisten Regierung

To sai dai kafafen yada labarun kasar sun ba da rahotannin da ke nuni da cewa a yau ne aka shirya yin wata ganawa tsakanin shugaba Moncef Marzouki da Rashid Gannoushi, shugaban jam'iyyar Ennnahda da ke mulkin kasar. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya nuna damuwarsa game da halin da ke wakana a wannan kasa ta arewacin Afirka yana mai cewa Tunisiya ta na tsintar kanta a cikin mawuyacin hali. Westerwelle da shugaban majalisar dokokin Kungiyar Tarayyar Turai, Martin Schulz sun yi kira ga bangarorin kasar da rikicin ya shafa da su yi aiki tare domin samar da ci gaban kasar.

A jiya Talata ne firaiministan Jebali da ake wa kallon mai matsakaicin ra'ayi ya yi murabus bayan da ya kasa cimma bukatarsa ta kafa gwamnati mai kunshe da kwararru.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar