Tunisiya ta sha alwashin yaƙi da ta′addanci | Labarai | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tunisiya ta sha alwashin yaƙi da ta'addanci

Shugaban ƙasar Beji Caid Essebsi ya ce za su yaƙi 'yan ta'adda bayan hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai a kan wani gidan addana kayan tarihi da ke a Tunis.

Shugaban na Tunisiya ya ce za su ƙara saka haNzari ga jami'an tsaro da kuma abin da ya shafi harkokin tsaro, domin daƙile yunƙurin 'yan ta'addar.

Hare-haren waɗanda aka kwashe tsawon sa'oi huɗu ana kai wa, mutane 19 suka mutu.17 daga cikinsu 'yan ƙasashen waje 'yan yawan shakatawa,biyu 'yan Tunisya,
a ciki har'da 'yan ƙasar Japan guda uku da 'yan Italiya suma uku da kuma 'yan ƙasar Spain guda byu da dai sauransu.