1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hade wasu ma'aikatu a Tunisiya

Zulaiha Abubakar
August 31, 2018

Firaiministan kasar Tunisiya Youssef Chahed ya sallami Ministan makamashi tare da wasu ministoci hudu daga aikin nan take bisa zargin su da cin hanci.

https://p.dw.com/p/346Q8
Tunesischer Premierminister - Youssef Chahed hält Ansprache in Tunis
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Sanarwar ta kara da cewa daukar wannan mataki ya zama wajibi sakamakon samun su da hannu wajen badakalar bayar da lasisin aikin hako mai tun a shekara ta 2009 ba bisa ka'ida ba. A wani sabon labarin kuma shugaban kasar ya hade ma'aikatar makamashin kasar da ta masana'antu a cigaba da daukar matakin yaki da cin hanci lamarin da yake kara karya tattalin arzikin kasar.