1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An yi sabuwar gwamnati a Tunisiya

Abdoulaye Mamane Amadou
October 11, 2021

Sabuwar majalisar ministoci a Tunisiya ta karbi rantsuwar kama aiki, makwanni bayan da shugaba Kais Saied  ya rusa majalisar dokoki tare da mallaka wa kansa karfin iko, lamarin da ya hadasa cece-kuce..

https://p.dw.com/p/41XMd
Tunisien Neue Regierung
Hoto: Tunisian presidency/dpa/MAXPPP/picture alliance

A yayin da take karbar rantsuwar kama aiki, Firaminista Najla Bouden mai shekaru 61, ta yi alkawarin fito na fito da cin hanci da rashuwa da ke neman yin nakasu ga harkokin tattalin arzikin kasar . A jawabinsa gaban sabuwar majalisar ministocin, Shugaba Saied ya ce ya dauki matakin ne da zummar tsamo Tunisiya daga fadawa cikin kangi, kana kuma hakan ka iya zaman hanya ta kaucewa wadanda ke son amfani da mukamansu dan wawushe dukiyar kasa.

Wannan ne karon farko a Tunisiya da mace za ta kasance shugabar gwamnati, matakin da kuma kungiyoyin kare hakin mata suka bayana a matsayin ci gaba, a kasar da yanzu hakan ke fama da matsin tattalin arziki mafi muni a yankin arewacin Afirka.