Tunisiya: An kafa dokar hana fitar dare
January 22, 2016Talla
Ma'aikatar cikin gidan Tunisiya din ce ta bada sanarwar wannan doka ta hana fita wadda za ta yi aiki tsakanin karfe 8 na dare zuwa biyar na Asuba kuma za ta fara aiki ne daga yau Juma'a.
Mai'aikatar ta ce ta dau wannan matakin ne duba da irin hadarin da ke akwai na afkawa mutane da kuma dukiyoyinsu. To sai dai wani matashin ya ce dokar ba za ta hana su bore ba don a cewarsa ''gwamnati za ta sauraremu ne kadai in muka yi bore. Tun shekaru biyar da suka gabata muka mika mata bukatunmu amma har yanzu ba ta sauraremu ba.''