1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika harabar kotun makil

Zainab Mohammed AbubakarJune 30, 2015

A wannan Talatar ce aka gurfanar da mutane 24 da ake zargi da kisan gilla wa fitaccen shugaban adawar kasar Tunisiya a Chokri Belaid a shekara ta 2013.

https://p.dw.com/p/1FqAq
Demonstrationen in Tunis am 16.03.2013
Hoto: Reuters

Wajen lauyoyi 200 da jami'ian 'yan sanda masu farin kaya da 'yan jarida ne suka halarci zaman kotun a birnin Tunis, a yayin da daruruwan mutane ke zanga-zanga a kofar harabar kotun.

A ranar 6 ga watan Febrairun shekarata 2013 ne dai aka bindige Belaid a kofar gidansa, mutumin da ke kakkausar suka ga gwamnatin jam'iyyar Ennahada da ke mulki a wancan lokaci. Kisan gilla da aka yi wa Belaid, ya jagoranci zanga-zanga da riginmun siyasa da ya kai ga rushewar gwamnatin Fraiminista Hamadi Jebali. Watanni biyar bayannan ne kuma, kasar ta Tunisia ta kara fadawa rikicin siyasa, sakamakon kisan gilla da aka kara yi wa wani shugaban adawa Mohammed Brahmi.

Duk da cewar 'yan jihadin Tunisiyan sun dauki alhakin hallaka Belaid, a wani somamen 'yansanda a watan Febrairun 2014, hukumomin kasar sun sanar da kashe mutumin da ake zargi da kisan gillar. Sai dai Iyalan Belaid na ci gaba da fafutukar ganin cewar gaskiya ta bayyana kan kisan na shi.