1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miyagun kwayoyi na neman zama ruwan dare a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
June 25, 2021

Ranar 26 ga watan Juni rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin waiwaye kan yaki da safara da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi a duniya.

https://p.dw.com/p/3vZsk
Pills, Pillen, Tabletten, Gesundheit, Health
Hoto: picture-alliance/TravelLightart/P. Trummer

A Jamhuriyar Benin, amfani da Tramadol ba tare da kima ba na illata kiwon lafiyar wasu matasan arewacin kasar. A cikin manyan garuruwan kasar har da yankunan karkara, muggan kwayoyin da ke sa maye irin su Tramadol da sauransu na yin mumman tasiri a zamantakewar matasan kasar. Wasu na kallonsa a matsayin kara kuzari don samun karfin yin kogado, yayin da wasu ke daukarsa a matsayin huce takaici idan aka shiga cikin wani mummunan hali. A takaice dai wannan maganin rage radadin ya zama samfurin da aka fi amfani da shi a  halin yanzu, musamman a tsakanin matasa.

Kalzium-TablettenKalzium-Tabletten
Hoto: Colourbox

Sai dai sayar da shi ta haramtacciyar hanya da kuma shan shi ba tare da ka'ida ba, ya ragu a cikin 'yan shekarun nan sakamakon farautar masu saye da masu sayar da muggan kwayoyi da hukumomin Jamhuriyar Benin ke yi a kan akan titi. Dama kuma sun aiwatar da sauye-sauye a fannin shagunan sayar da magani da cibiyoyin hada magunguna a kasar.

A tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2020 kadai, an kame ton 100 na kwayoyin sa maye na tramadol. Amma kuma bai sa matsalar shaye-shayen ta kau baki daya ba. a maimakon haka ma dai, shaye-shayen na dada karuwa a wasu yankuna, musamman a arewacin Jamhuriyar ta Benin, kamar yadda Rémi Biaou, shugaban kungiyar 'yan acaba a Parakou da ke arewacin Benin ya bayyana.

“Tramadol wani samfuri kwaya ne da mutane da yawa ke amfani da shi a wannan garin don buguwa, kuma suna fada cewa suna sha ne domin ya taimaka musu faranta wa kansu rai, ko kuma don samar wa kansu karfin gwiwa na iya yin aiki da kyau".

Wasu lokutan dai, masu amfani da Tramadol na hada shi da wani nau'in kayan maye kafin su dirka. Wannan shi ne abin da Adamou Idriss Silla, shugaban gundumar farko ta Parakou ya bayyana.

Medikament Tramadol
Hoto: Imago Images/Le Pictorium/J. Schmidt-Whitley

“Akwai samfurin da ake kira ''Worou'', ana samar da shi ne daga wani nau'i na ganye. A cewar wadanda suka saba amfani da shi, idan ka dauki dan kadan ka hada da Tramadol wanda aka gauraya da ganyen, sai ya mayar da mutum tamkar inji sarkin karfi. "

Sai dai yawan maimaita shan kayan mayen na habaka jarabar amfani da shi a gurin yawancin masu amfani da wannan samfurin, a cewar Mireille Adjinda, masaniniyar halayyar dan Adam a birnin Cotonou.

"Suna amfani da jikinsu har su kure shi, kuma sun yi imanin cewa duk lokacin da suka yi aiki da ya wuce kima, za su samu kudin shiga mai yawa. Don haka kokarin da suke yi na amfani da karfi, suna son kwantar da tsukun kwanjin da suke fuskanta a jikinsu. saboda haka suke amfani da Tramadol wanda yake ba su wannan nau'i na jin dadin, lamarin da ke tunzura su zuwa ga amfani da su a rayuwar yau da kullun. Amma, kash, ba sa ganin sakamakon na dogon lokaci. "

Togo Drogenabhängigkeit Schmerzmittel Opioide  Lome
Hoto: DW/L. Salm-Reifferscheidt

A asibitin kwararu da cibiyar tabin hankali na jami'ar Cotonou ne ake bayar da kulawa ga mutanen da shaye-shaye ko hadiye-hadiyen kayan maye shigen su Tramadol ya dagulawa lissafi ko kuma ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Wannan dai shi ne asibitin tabin hankali daya tilo a cikin Benin, inda Dr. Elvire Klikpo ke aiki. Kwararren masanin shaye-shayen miyagun kwayoyin ya bayyana cewa ana kula da wadanda ba su yi nisa a shaye-shayen ba nan take, yayin da ake kwantar da wadanda shaye-shayensu ya kai intaha.

 “Wasu mutane ana kulawa da su a asibiti, ma’ana suna zuwa neman shawararwari kuma su koma gida. Wasu kuma ana kwantar da su a asibiti saboda suna bukatar kulawa ta  musamman ta yau da kullun. Abu ne da muke yi anan kuma asibitin namu yana da sashe da ke kula da masu shan kwayoyi. "

Cibiyar CNHU da ke kula da masu tabin hankali yana tsara shirye-shiryen ilimantarwa da wayar da kan jama'a game da illar amfani da wasu maguguna da wasu kayayyakin maye kamar Tramadol.