Tunawa da rasuwar Nelson Mandela | Labarai | DW | 05.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tunawa da rasuwar Nelson Mandela

A wannan Jumma'ar ce biyar ga watan Disamba 2014, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya cika shekara guda da rasuwa.

Da yake magana a jajibirin wannan rana Bishop Desmond Tutu, ya yi kira ga al'umma kasar Afirka ta Kudu da su yi koyi da halayan marigayin wanda yake gwarzon yaki da wariyar launin fata a wannan kasa , inda ya kara da cewa abin da yake tilas a gare su wajan Madiba, shi ne su ci gaba da kasancewa irin al'ummar da yake tunanin gani a kullum, tare da yin koyi da kyawawan halayansa, ta yadda za su kasance al'umma mai mutunta hakkokin dan Adama, tare da rayuwa cikin mutunci dan kyautata gobe.

Marigayi Nelson Mandela dai ya rasu ne a ranar biyar ga watan Disamba na 2013 bayan da ya yi fama da dogon rishin lafiya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo