1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da mutuwar Martin Luther King

Abdullahi Tanko Bala
April 4, 2018

Jama'a na ci gaba da yin dandazo a Memphis jihar Tennesse a Amirka inda aka kashe Martin Luther King Jnr, a ranar 4 ga watan Aprilun 1968 shekaru 50 cif a yau domin tunawa da rayuwarsa.

https://p.dw.com/p/2vRto
Civil Rights March on Washington, D.C.
Hoto: National Archives and Records Administration/Marina Amaral

A shekara 1968 Martin Luther King ya jagoranci zanga zangar ma'aikatan tsabtar muhalli a Memphis Jihar Tennesse ta Amirka domin neman karin albashi da kyautatuwar yanayin aiki inda kuma tarzoma ta barke tsakanin masu zanga zangar da jami'a tsaro.

Da yammacin jajiberen zanga zangar ce Martin Luther ya gabatar da gagarumar hudubar da ta yi shura a mujami'ar Mason Temple inda ya yi tsokaci yana cewa ya hangi kyakkyawar makoma ta kasa mai yalwa a gaba. 

Muna da kalubale a gaba amma wannan bai dame ni ba saboda na kai kololuwar tsauni. Kamar kowane mahaluki zan so na yi tsawon rai amma wannan ba shi ne a gaba na ba a yanzu. Ba lallai ne na kai wannan lokaci tare da ku ba, to amma ina so ku sani a wannan dare a yau cewa a matsayinmu na al'umma zamu kai wannan matsayi da izinin Allah.