Tuna sanannen gwarzon kwallon kafa Eusebio
Shine ya sami lambar farko ta dan kwallo mafi gwaninta a wasannin kofin duniya na 1966, inda ya ci kwallo 9 ya kuma shiga tarihin Portugal. Eusebio da Silva Ferreira ko Eusebio haifaffen Mozambik ya rasu da shekaru 71
Sanannen gwarzo a Lisbon
Mutum-mutumin Eusebio dake tsaye a gaban filin wasan Estadio da Luz na Benfica a Lisbon tun daga Lahadi ya zama dandalin haduwar jama'a, inda masu sha'awarsa suke ta ajiye masa kayaiyakin tunawa. Eusebio ya dauki mafi yawan zamaninsa na kwallon kafa ne yana wasa a kungiyar Benfica inda yaci kwallo fiye da 300, wato fiye da cin kwallo daya ga ko wane wasa da yayi wa Benfica
Ya sami lambar farko ta dan wasan da yafi cin kwallo
Eusebio ya ci kwallo tara a wasannin kofin duniya na 1966, ciki har da ci 3-1 kan Brazil. To amma wasansa tsakanin Portugal da Korea Ta Arewa ne ya shiga kundin tarihi. Lokacin da aka ci Portugal 3, Eusebio ya jefa kwallo sau hudu a rabi na 2 na wasan, inda a karshe Portugal ta sami nasara daci 5-3. To sai dai Ingila tafi karfin kungiyar ta "Black Panther" a wasan kusa da na karshe.
Daga mummunan talauci ya zuwa ga yin suna a duniya
Eusebio an haifeshi ne a kasar da a yanzu aka santa da sunan Mozambik, inda ya taso cikin mummunan talauci. Lokacin da ya cika shekaru 18 da haihuwa, kungiyar Benfica Lisbon ta dauke shi zuwa Portugal, inda ya yi wasa tare da matukar nasara tsawon shekaru 15. Eusebio ya mutu ranar Lahadi a babban birnin na Portugal, wato a gida bayan rayuwar shekaru 71 a duniya.
Nasarorin wasan kwallon kafa da Benfica Lisbon
Eusebio ya sami nasaori da dama dauke da rigar Benfica, abin da ya hada da daukar garkuwar zama zakara a Lig sau 11. A wasannin Turai ya ci kwallon da ya baiwa Benfica nasara a wasan neman daukar kofin Turai kan Real Madrid. Shekara guda bayan hakan ya sake cin kwallo a wasan karshe kan kungiyar AC Milan, ko da shike Benfica bata sami nasarar wasan ba.
Manyan gwanaye biyu: Eusebio da Gerd Müller
A 1973 Eusebio ya sami lambar yabo ta kasashen Turai da ake baiwa dan wasan da yafi kwazo a wasannin kungiyoyi. Ya sami lambar bayan da ya kayar da dan takara Gerd Müller na Jamus. Manyan yan wasan biyu sune suka mamaye wasannin lig na kasashensu. Müller da Bayern Munich, Eusebio da Benfica Lisbon.
Gwarzo a kasarsa
Eusebio ya sami daukaka a ko ina a Portugal da kasarsa ta haihuwa Mozambik. Kungiyar Benfica, inda ya dauki mafi yawan lokacinsa na kwallon kafa, ta kirkiro wata takara dake amsa sunansa da ake yi a watan Agusta na ko wace shekara. A takarar baya-bayan nan, Eusebio ba da son ransa ba, ya mika kofin dake amsa sunansa ga yan wasan Sao Paulo na Brazil, wadanda suka kayar da Benfica da ci 2-0.
Saanannun fuskoki
Sanannen dan wasan ya kasance cikin annashuwa a lokacin wasan karshe na cin kofin Turai(European League) a watan Mayu na 2013, lokacin da Benfica da Chelsea suka kara da juna. A hoton ana iya ganinsa da shugaban Uefa Michel Platini(tsakiya) da tsohon dan wasan Holand, Johan Cruyff. To amma Eusebio ya yi fama da mummunan rashin lafiya a 'yan shekarun nan, kuma an sha jiyyarsa saboda ciwon huhu.
Yan wasan Portugal sun yabi Eusebio
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo shima yana zaman juyayi. A 2011 Ronaldo ya karbi lambar yabo ta dan wasa mafi kwazo daga hannun Eusebio(hoto). A shafinsa na Twitter Ronaldo ya rubuta: "ba zamu manta da kai ba." Tsohon dan wasan Portugal, Luis Figo yace "wannan babban rashi ne garemu." Mai koyar da Chelsea, Jose Maurinho yace ya dauki Eusebio a matsayin wanda zai ci gaba da rayuwa har abada.