1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An baiyana tuhumar Amirka kan Assange

Abdullahi Tanko Bala
November 16, 2018

A bisa kuskure an baiyana takadar tuhumar da Amirka ke yi wa Julius Assange mai shafin kwarmata bayanan sirri wikiLeaks kan zargin tona asirin Amirka.

https://p.dw.com/p/38Pwq
Julian Assange
Hoto: Reuters/P. Nicholls

Masu gabatar da kara na Amirka sun sanar da wanzuwar takardar tuhumar Julian Assange wanda shafinsa na yanar Gizo da ke kwarmata bayanan sirri Wikileaks ya fallasa wasu baiyanan sirri da suka yi kaurin suna na gwamnatin Amirka a shekarar 2010.

Sanarwar takardar tuhumar ta biyo bayan kuskuren gabatar da wata takarda ce ta kara da mukaddashin mai gabatar da kara na Amirka Kellen Dwyer ya yi ne a ranar Alhamis inda ya bukaci adana tuhumar ta Assange cikin sirri.

Ya kuma ce za a cigaba da adana tuhumar har sai an kama Assange din. Babu tabbas kan tuhumar da Assange din zai fuskata wanda har yanzu yake makale a ofishin jakadancin Equador a London tun shekarar 2012