Tsugunne ba ta ƙare ba a ƙasar Kenya | Siyasa | DW | 11.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsugunne ba ta ƙare ba a ƙasar Kenya

Raila Odinga ya shigar da ƙara domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Raila Odinga, Prime Minister of Kenya, makes a point at a session called, More voting, less Democracy, during the second day of the World Economic Forum on Africa on May 5, 2011, in Cape Town, South Africa. African economies are among the world's fastest-growing but leaps in output have not been a silver bullet for better living standards, delegates at the World Economic Forum said Thursday. AFP PHOTO/RODGER BOSCH (Photo credit should read RODGER BOSCH/AFP/Getty Images)

Raila Odinga

Babbar Jam'iyyar adawa ta ƙasar Kenya wato CORD, wadda kuma itace Jam'iyyar Firaminsta Raila Odinga ta yi ƙorafin cewa bata samu haɗin kan da ya kamata daga Hukumar Zaɓen ƙasar ba,domin ta shiryawa ƙalubalantar sakamakon babban zaɓen da aka gudanar cikin makon daya gabata a Kenyan.

Da yake watsi da sakamakon zaɓen Firaminista Raila Odinga yace Demokraɗiyyar ƙasar Kenya na kan matakin gwaji ne.

Tun dai a matakin ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa jam'iyyar Odinga tayi ƙorafin cewa akwai kura-kurai tare kuma da yin kira da ayi gyara akai.

President-elect of Kenya Uhuru Kenyatta (C) with his wife Margaret (R) waves to his supporters in front of a church in his hometown Gatundu March 10, 2013. Uhuru Kenyatta, indicted for crimes against humanity, was declared winner of Kenya's presidential election on Saturday, but rival Raila Odinga said he would challenge the outcome in court and asked supporters to avoid violence. REUTERS/Marko Djurica (KENYA - Tags: POLITICS ELECTIONS)

Uhuru Kenyatta saban shugaban Kenya da tawagarsa

A jawabansu da suka yi Ministan Ilimi na Kenya Mutula Kilonzo da kuma Ministan Kula da al'amuran Filaye James Orengo, sun yi ƙorafin cewa dama akwai manaƙisa da aka shirya domin baiwa mataimakin Firaministan Uhuru Kenyatta nasara a zaɓen, inda suka yi ƙorafin cewa Hukumar zaɓen ƙasar ta ƙi amincewa da buƙatarsu ta damawa da su yayin yin rijistar masu kaɗa ƙuri'a.

Kotun ƙolin ƙasar dai ta bayyana cewa a shirye take ta saurari duk wani ƙorafi da za'a gabatar a gabanta kan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon jiya, cikin hanzari da kuma adalci.

Wani lauya a ƙasar ta Kenya Bobby Mkangi, yace in har Jam'iyyar Firaminsta Raila Odinga ta gabatarwa da kotu gamssassun shaidu tana iya samun nasara.

"Nasarar da Raila Odinga zai samu a Kotu ta dogara ne kan shaidun da ya gabatar a gaban ta, in har shaidun da zai gabatar sun gamsar da kotu to zai samu nasara kuma al'ummar ƙasar Kenya sun zuba ido su ga irin shaidun da Odinga zai gabatar wa kotun".

Kenyan Vice President Kalonzo Musyoka addresses supporters in Nairobi on December 4, 2012 after agreeing with Prime Minister Raila Odinga and Trade Minister Moses Wetangula to form a powerful alliance as running mates in presidential elections due in March 2013. The former rivals along with leaders of 10 other smaller parties, signed an agreement in front of thousands of supporters to form the Coalition for Reform and Democracy (CORD) party. Odinga is widely tipped to be the presidential candidate with Musyoka as his deputy, although no formal announcement was made. AFP PHOTO / TONY KARUMBA (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP/Getty Images)

Raila Odinga

Ya kuma bayyana cewa, kotun ƙolin ƙasar ta kwashe tsawon watanni t ana shirya yadda zata tunkari ƙorafe -ƙorafen bayan zaɓe da za'a shigar a gabanta.

Yace "Kotun ƙoli tana sane kuma a shirye take kan cewa ɗaya daga cikin 'yan takara ka iya ƙalubalantar zaɓe kuma ta baiwa al'ummar ƙasa damar su ƙalubalanci zaɓen da aka gudanar a ƙasar kenya sun daɗe suna shirin karɓar wadan nan ƙorafe -ƙarafe kuma suna da damar yin ƙorafine cikin kwanaki 14 da gudanar da zaɓen kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada".

Shima wani shugaban cibiyar nazarin kimiyar siyasa da haƙƙin bani Adama dake ƙasar Kamaru Alain Didier Olinga ya bayyana nasa ra'ayin dangane da wanna zaɓen

"Al'umar Kenya sun zaɓi 'yan takarar da suka fi dacewa gare su.Ta na iya yiwuwa sammacin da kotin ICC ta yi kan Uhuru Kenyatta ya taimaka masa wajen samun nasara.To amma ko da ya na kan karagar mulki, kotin ICC na da 'yancin gurfanar da shi. Saboda a tsarin doka kotun na iya tuhumarsa saidai aikatawa a zahiri shine matsala."

Tun dai gabanin zaɓen ƙasashen Amurka da kuma sauran ƙasashen Yamma dake zaman manyan waɗanda ke bada tallafi ga ƙasar ta Kenya sun bayyan cewa lashe zaɓe ga Uhuru Kenyatta ka iya wargaza alaƙar diplomasiyya tsakanin abokan yankin kan yakin da su keyi da masu tada ƙayar baya.

Uhuru Kenyatta da wanda ke mara masa baya a matsayin mataimakinsa William Ruto na fuskantar Tuhuma daga kotun hukunta masu aikata laifukan yaƙi ta ƙasa da ƙasa, zargin da dukkansu suka ki amincewa da shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Jaafar
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin